Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Rasha Sergey Naryshkin a dakin babban taron jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing.
Yayin ganawar ta su a yau Alhamis, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, bunkasuwar dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Rasha a dukkan fannoni, ta dace da burin jama'ar kasashen, da bukatun su na samun bunkasuwa, da kuma yanayin samun zaman lafiya da ci gaba, da hadin gwiwar moriyar juna a fadin duniya gaba daya.
A nasa bangare, Sergey Naryshkin ya isar da gaisuwar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zuwa shugaba Xi. Ya kuma bayyana cewa Rasha na sanya dangantakar dake tsakanin ta da kasar Sin a sahun farko, a fannin mu'amalar diplomasiyya. (Zainab)