in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tura sakon taya murnar kaddamar da taron ministoci karo na 7 na dandanlin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa
2016-05-12 20:24:05 cri
A yau Alhamis, shugaban kasar Sin ya tura wani sakon taya murnar kaddamar da taron ministoci karo na 7 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa da ke gudana a Doha, hedkwatar kasar Qatar.

A cikin sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, a yayin wannan taron ministocin, za a tabbatar da muhimman fannoni da shirye-shirye da kasar Sin da kasashen Larabawa za su aiwatar tare cikin hadin gwiwa. Sakamakon haka, wannan taro yana da muhimmanci sosai ga kokarin bullo da tsarin yin hadin gwiwar moriyar juna da karfafa yin mu'amala a fannin abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum.

Sannan, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin tana son hada kai da kasashen Larabawa wajen bunkasa shirin nan na "ziri daya da hanya daya" bisa ka'idojin "yin tattaunawa tare, da neman ci gaba tare da kuma cin gajiyar sakamako tare", ta yadda za a bunkasa huldar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa kamar yadda ake fata.

Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin da takwaransa Sheikh Mohammed bin Abdulrahman na kasar Qatar, da Nabil Elaraby, babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa sun halarci bikin kaddamar da taron. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China