A madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da shi kansa, Xi Jinping ya taya murna ga Kim Jong-un game da sabon ci gaba da aka samu a kasar dake karkashin shugabancin jam'iyyar kwadago ta kasar wajen raya kasar bisa tsarin kwaminisanci na zamani.
Xi ya bayyana cewa, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatin kasar suna dora muhimmanci sosai game da alakar dake tsakanin kasashen biyu. Yana kuma fatan yin kokari tare da kasar Koriya ta Arewa, domin inganta hadin gwiwar sada zumunta da ke tsakanin kasashen biyu, don kawo alheri ga kasashen biyu da jama'arsu, tare kuma da ba da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da karko da samun bunkasuwa a shiyyar.(Bako)