in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da sarki Mohammed VI na kasar Morocco
2016-05-11 21:19:46 cri

A yau ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da sarki Mohammed VI na kasar Morocco a nan Beijing, inda suka tsai da kudurin kulla huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma bisa ka'idojin zaman daidai wa daida da moriyar juna da mutunta juna, ta yadda za a bude wani sabon shafi a huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, kasashen Afirka da na Larabawa sun kasance aminan arziki na kasar Sin a lokacin da take neman ci gaba. A yayin taron koli na dandanlin tattaunawar hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka da aka gudanar a karshen shekarar bara a Johnnesburg na kasar Afirka ta kudu, shugaba Xi ya gabatar da "shirye-shirye 10 na yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka". Sannan a yayin da yake ziyarar yankin Gabas ta tsakiya a watan Janairu na bana, shugaban na Sin ya gabatar da sabbin jerin matakan yin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa domin bunkasa shirin nan na "ziri daya da hanya daya" tare, ta yadda za a cimma burin samun ci gaban kasar Sin da kasashen Larabawa gaba daya. Kasar Sin na maraba da kasar Morocco da ta halarci hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa domin kara bullo da sabbin matakai a kokarin bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren kuma, Sarki Mohammed VI ya bayyana cewa, kasarsa tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin domin karfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fannonin cinikayya da tattalin arziki da kuma samar da kayayyakin more rayuwar jama'a. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China