Taron mata na kungiyar G20 bangare ne na taron kolin kungiyar G20, wanda aka yi wa taken "halartar taro cikin adalci, yayin da neman bunkasuwa ta sabbin hanyoyi". Haka kuma, wakilai kimanin dari biyu daga mambobi kasashen kungiyar G20, da wasu kasashen da aka gayyata tare da wasu kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa sun halarci taro.
A jawabin da ya gabatar, Li Yuanchao ya bayyana cewa kamata ya yi kasashe mambobin kasashen G20 su tsara shirin neman bunkasuwa, da sabunta manufofi, da sanar da adalci ga mata, da kuma shigar da su cikin yunkurin samun ci gaba.
A nata bangare kuma, Shen Yueyue ta ce, tarayyar mata ta kasar Sin na fatan gudanar da hadin gwiwa da matan kasashen duniya, wajen neman sabbin hanyoyin musayar al'adu da shawarwari na wanzar da ci gaba cikin hadin gwiwa. (Maryam)