Rahotanni na cewa, an kai hare-hare da boma-bomai sau uku a birnin Tartus, wadanda suka haddasa mutuwar mutane a kalla 20.
A wannan rana da safe, wasu boma-bomai sun fashe a asibiti da hukumar kula da samar da wutar lantarki da wata tashar motoci a birnin Jableh, ya zuwa yanzu hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 45.
Daga bisani kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai hare-haren boma-bomai da aka kai a biranen Tartus da Jableh. (Zainab)