in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Syria sun harbe wasu dakaru masu tsatsauran ra'ayi
2016-05-19 13:53:03 cri
Rahotanni daga kasar Syria na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar harbe wasu dakarun kungiyar IS da na kungiyar Jabhat al-Nusra,sakamakon matakan sojan da sojojin suka dauka a wurare daban daban na kasar a jiya Laraba.

Haka kuma, an halaka wasu dakarun kungiyar IS sakamakon wasu hare-hare ta sama da sojojin gwamantin kasar suka kai a gabashin lardin Homs. Bugu da kari, sojojin sun harbe dakarun kungiyar Jabhat al-Nusra 15 a yankin gabashin lardin Deraa, a sa'i daya kuma, dakarun kungiyar IS 20 sun mutu sakamakon harin da sojojin gwamnatin kasar suka kai musu a lardin Deir ez-Zor da ke yankin arewa maso gabashin kasar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China