Labarin ya ambato bangaren soja na cewa, sojojin gwamnati sun dauki matakin soja kan yankin dake kudancin Hama, inda suka kawar da kangiya da kungiyoyin biyu suka yi a wani kamfanin samar da wutar lantarki dake wurin. Matakin da sojojin gwamnati suka dauka ya taimaka wajen harbe dakaru 125 har lahira.
An ce, a kwanan baya kungiyoyin Al-Nusra da Ahrar al-Sham sun kai farmaki kan garin Zara dake kudancin Hama, inda suka kashe wasu mazauna wurin da kuma yin garkuwa da wasu.
A ranar 22 ga watan Faburarun, kasashen Amurka da Rasha sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin da rikicin ya shafa na kasar Syria, wadda ta soma aiki a ranar 27 ga watan Faburairu, amma yarjejeniyar din ba ta shafar matakan soja na murkushe kungiyoyin ta'addanci da kwamitin sulhu na MDD ya tabbatar, ciki har da kungiyoyin IS da Al-Nusra da dai sauransu. (Bilkisu)