Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar AU, ta yi tur da hallaka jami'in cikin wata sanarwar da AU ta fitar a ranar Talatar data gabata.
Marigayi birgediya janar Kararuza, shi ne tsohon mataimakin babban kwamandan tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriya tsakaiyar Afrika CAR (MISCA), kuma jami'in kwamitin wanzar da zaman lafiya na MDD a CAR (MINUSCA).
Sanarwar ta ce, mai dakin marigayi birgediya janar Kararuza ma ta rasa ranta a lokacin harin, sannan wata 'yar sa ta samu munanan raunuka.
Dlamini-Zuma, ta aike da sakon ta'aziyya a madadin AU ga iyalan marigayin tare da yin fatar samu sauki ga diyar tasa.
Madam Dlamini-Zuma, ta ce ana ta fuskantar munanan hare hare a 'yan kwanakin nan, kuma akwai alamun rikicin zai iya bazuwa zuwa ga sassan kasar ta Burundi har ma da kewayen kasar.
AU ta bayyana hare haren a matsayin cin zarafi ga rayuwar bil adama sannan ta bukaci a gudanar da bincike domin gano wadanda keda hannu don hukunta su. (Ahmad Fagam)