Mista Willy Nyamitwe, babban mai bada shawara na fadar shugaban kasar Burundi, da ke kula da harkokin sadarwa, ya jaddada cewa wadanda suka salwantar da rayuwar 'yan kasa, da kuma suka nemi kifar da hukumomin kasa da aka zabe su ta hanyar demokaradiyya da sauransu da suka shiga tawaye da makamai a cikin kasar ba za a iya gayyatarsu ba a cikin wannan tattaunawa ta tsakanin 'yan kasar Burundi. (Maman Ada)