in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. 5 a Mali
2016-05-19 14:18:39 cri
A daren ranar 18 ga watan nan ne ofishin magatakardar M.D.D. ya bayyana cewa, an kai hari ga sojojin kiyaye zaman lafiya na M.D.D. da ke kasar Mali a yankin Kidal, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 5, tare da jikkatar wasu 3.

Game da hakan, sakatare janar na M.D.D. Ban Ki-Moon ya fidda wata sanarwa, inda ya yi Allah-wadai da lamarin, kuma ya yi kira da a gabatar da wadanda suka aikata wannan ta'asa gaban kuliya.

Sanarwar ta ce bisa kwarya-kwaryar labarin da aka samu, an ce an kai harin bom ga ayarin motoci na sojojin samar da zaman lafiya ta M.D.D. da ke kasar Mali, a wani wuri da ke da nisan kilomita 15, a arewa da birnin Aguelhok da ke yankin Kidal, harin da kuma ya hallaka sojoji 'yan asalin Chadi 5.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China