in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta halarci muhawara a babban taron MDD bisa matsayin koli kan tabbatar da dauwamammen ci gaban duniya
2016-04-22 10:00:06 cri
Daga ranar 19 zuwa 21 ga wata, mataimakin ministan harkokin waje na Sin, kana mai kula da harkokin kungiyar G20 a bangaren Sin, mista Li Baodong ya halarci muhawara a babban taron MDD bisa matsayin koli kan tabbatar da samun dauwamammen ci gaban duniya, taron da aka gudanar a birnin New York, tare da yin shawarwari da kungiyar G77 kan batun share fagen gudanar da taron koli na kungiyar G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin.

A yayin da yake jawabinsa a gun muhawarar, Li Baodong ya yi kira ga bangarori daban daban da su tabbatar da gudanar da shirin samun dauwamemmen ci gaba na shekarar 2030 a duk fannoni. A watan Satumban bara, shugaba Xi Jinping ya yi alkawarinsa a gun taron kolin MDD cewa, Sin za ta yi kokari tare da sauran kasashen duniya domin gudanar da wannan shiri yadda ya kamata.

Ban da haka, Li Baodong ya kara da cewa, a matsayin shugaban kungiyar G20 na bana, Sin tana kokarin sa kaimi ga kungiyar G20 wajen ba da gudummawa kan zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa da tabbatar da gudanar da shirin samun dauwamemmen ci gaba na shekarar 2030. Dadin dadawa, Sin ta yi kira ga kungiyar G20 da ta nuna goyon baya ga kasashen Afirka da kasashe mafi fama da talauci wajen raya masana'antunsu, tare da yin hadin gwiwa da su a wannan fanni. Bisa kiran da Sin ke yi, kungiyar G20 ta gabatar da sanarwa kan sauyin yanayi a karon farko, har ma bangarori daban daban sun yi alkawarin rattaba hannu kan yarjejeniyar Paris, tare da kokarin aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Bangarori daban daban sun nuna babban yabo kan hanyar da Sin ke bi wajen gudanar da tarurukan bisa ra'ayin bude kofa, da gudanar da kome a bayyane, da kuma yarda da ra'ayoyi daban daban, tare da nuna babban yabo ga Sin kan yadda take sauraron muryoyin kasashe masu tasowa. Sun yi niyyar nuna goyon baya ga kasar Sin wajen gudanar da tarurukan, tare da fatan samun kyakkyawan sakamako a gun taron koli da zai gudana a birnin Hangzhou.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China