in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta kaddamar da sabbin ayyukan dangantaka guda 10 tare da kasar Congo
2016-04-27 11:16:33 cri
Tawagar kungiyar tarayyar Turai (EU) dake kasar Congo, ta kaddamar a ranar Talata a birnin Brazzaville, da wasu sabbin ayyukan raya al'umma da tattalin arziki guda goma da nufin kara kyautata zaman rayuwar mutane masu dan karamin karfi sosai. Wadannan ayyuka sun janyo tallafin kudi na fiye da kudin Euro miliyan 5.3, kwatankwacin Sefa biliyan 3.5 daga tsarin gidauniyyar "Masu ruwa da tsaki da ba na gwamnati ba da hukumomin yankuna ta fuskar cigaba" na kungiyar tarayyar Turai da kuma cibiyar tarayyar Turai kan demokaradiyya da 'yancin dan adam, wadanda suka kasance hanyoyin samar da kudade biyu na wannan hukuma. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China