Janar Olonishakin ya ce ko shakka babu, rundunar za ta fuskanci kalubalen da tsagerun kungiyar Niger Delta Avengers ke haifarwa a yankin, ko da yake a cewar sa ba ya ga dabarun yaki, rundunar za kuma ta tattauna da masu ruwa da tsaki a yankin, da nufin lalubo hanyoyin ba da kariya ga bututan mai da na iskar gas, wadanda ke matukar fuskantar barazana daga tsagerun yankin. (Saminu Hassan)