Jami'an da suka jagoranci taron su ne mista Lou Jiwei, ministan kudin kasar Sin, gami da mista Zhou Xiaochuan, shugaban baitulmalin kasar Sin. Haka kuma a wajen taron, manyan jami'an kasashe daban daban sun tattauna batutuwan da suka hada da yanayin tattalin arzikin duniya, da tsare-tsaren harkar kudi na kasa da kasa, da aikin zuba jari, da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashe daban daban don gudanar da aikin karbar haraji, gami da tattara kudi don yakar ta'addanci, da dai makamantansu.
Mahalarta taron suna ganin cewa, tattalin arzikin duniya na ci gaba da samun farfadowa, sai dai irin karuwar da ake samu ba ta da sauri, kuma akwai rashin daidaituwa tsakanin kasashe daban daban. Don haka ana fuskatar wani yanayi na rashin tabbas ta fuskar makomar tattalin arzikin duniya.(Bello Wang)