Game da wannan batu, a yayin taron dindindin na majalisar gudanarwar kasar Sin da aka shirya a kwanan baya, an tattauna batun kafa yankunan cinikayya ta fasahar yanar gizo na gwaji, da nufin bunkasa harkokin cinikayyar da ake yi da kasashen waje.
Amma a wani fanni na daban, idan ana so a bunkasa cinikin da ake yi da kasashen waje, kamata ya yi a mayar da hankali kan kayayyakin da ake fitar zuwa kasashen ketare. Wato a yayin da ake kokarin habaka hanyoyi, da kyautata tsari, a sa'i daya kuma ya kamata a kula da ingancin kayayyaki, da ba da hidima game da haka yadda ya kamata. (Bilkisu)