Gao Hucheng ya bayyana a gun taron manema labaru da ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar cewa, ana raya yankunan yin ciniki cikin 'yanci na gwaji yadda ya kamata, kana an samu nasarori game da batutuwan da suka shafi tsari, sassauta harkokin gwamnatoci, mika iko ga kananan hukumomi da dai sauransu.
Gao Hucheng ya kara da cewa, a kokarin da ake na sassauta harkokin ciniki, an bullo da wani tsarin musamman na cinikin kasa da kasa a yankunan yin ciniki cikin 'yanci, sannan yadda hukumar kwastan ta ke gudanar da ayyukanta ya karu da kashi 40 cikin dari, kuma saurin yana ci gaba da karuwa. (Zainab)