in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fadada hanyar ciniki ta yanar gizo a kasar Sin
2016-01-14 15:51:19 cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsaida kudurin fadada tsarin manufofin cinikayya ta hanyar yanar gizo a wurare daban daban na yankin cinikayya na gwaji da aka kafa a birnin Hangzhou na kasar Sin.

Sabon tsarin cinikin har da cinikayya ta hanyar yanar gizo a tsakanin kasa da kasa ya kasance batun dake jawo hankali sosai a harkokin cinikayyar waje na kasar Sin. Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin waje na ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin Wang Dongtang ya yi bayani cewa, daga shekarar 2015, saurin bunkasuwar yawan kayayyakin da Sin ta fitar ta hanyar cinikayyar yanar gizo zuwa kasashen waje ya karu da kashi 30 cikin dari ko fiye, wanda ya sa kaimi ga kanana da matsakaita kamfanoni wajen fitar da kayayyakinsu, wannan ya kasance muhimmin abun dake sa kaimi ga bunkasuwar cinikin waje na kasar Sin, kana ya ba da gudummawa wajen samar da aikin yi.

Ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ta yi hasashe cewa, yawan cinikin shigi da fici ta hanyar yanar gizo na kasar Sin a shekarar 2016 zai kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 6500, kana yawan cinikin a shekaru masu zuwa zai karu zuwa kashi 20 cikin dari bisa na dukkan cinikin kasar, kuma saurin karuwar cinikin a kowace shekara zai kai fiye da kashi 30 cikin dari. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China