A yayin da ake fama da matsin lamba a fannin cinikayyar shigi da fici, an dora muhimmanci sosai kan kasuwanci ta fasahar yanar gizo Internet a gun taron majalisar gudanarwar Sin na farko a shekarar 2016.
A gun wannan taro, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da shawarar kafa wata sabuwar tsangayar raya harkokin cinikayya ta fasahar yanar gizo Internet a tsakanin kasa da kasa, ta yadda za a rage kudaden da kanana da matsakaitan kamfannoni ke kashewa domin gudanar da harkokinsu.
Kafofin watsa labaru sun bayyana cewa, wannan shi ne karo na 4 da Li Keqiang ya nemi a inganta cinikayya ta yanar gizo Internet a gun taron majalisar gudanarwar kasar tun daga shekarar 2015.
Ya kuma nanata cewa, ya kamata a kyautata hidimar da ake samarwa ta hanyar amfani da yanar gizo. Don haka ake sa ran ganin, sana'ar cinikayya ta fasahar yanar gizo a tsakanin kasa da kasa tana da makoma mai kyau, kana za ta kawo moriya ga cinikayyar kasa da kasa da kuma kanana da matsakaitan kamfannoni.(Lami)