Jirgin ya bace ne a jiya Laraba da karfe 2 da minti 45 bisa agogon kasar Masar kafin kuma wasu kafofin yada labaru sun sanar da faduwarsa a Teku.
Kamfanin ya ce jirgin mai lamba MS804 samfurin Airbus A320 ne, yana kuma dauke da fasinjoji 59, da ma'aikata 10, ya bace ne yayin da yake tafiya cikin tsayin mita 11,277 a sararin samaniyar kasar ta Masar. A halin da ake ciki kamfanin jiragen saman na Masar ya sanarwa sassan da abun ya shafa aukuwar hakan, domin fara aikin lalubo inda jirgin ya shiga. (Bako)