in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a gano jirgin saman fasinja na kasar Masar da ya bace ba
2016-05-20 10:04:53 cri
A ranar 19 ga wata, cibiyar yada labaru na kamfanin zirga-zirgar jiragen saman kasar Masar ta bayyana cewa, tuni labarin da wannan kamfani ya bayar na cewa an samu tarkacen jirgin saman fasinjan kamfanin da ya ba ce, kuskure ne, kuma wani jami'in kasar Girka ya bayyana cewa, abubuwan da aka gani cikin teku a wannan rana ba sassan jirgin saman samfurin Airbus A320 ne ba.

Jirgin saman fasinjan da ya bace ya tashi daga birnin Paris zuwa birnin Alkahira dauke da fasinjoji 56, masu tsaro 3, da sauran ma'aikata 7, har zuwa yanzu, kasashen Masar da Girka na ci gaba da neman jirgin a tekunan da ke kewayen wurin da ake zaton jirgin ya fada.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China