Babban alkalin Masar, Hisham Barakat, ya mutu a yayin wani harin bam da aka dana ga mota a cikin watan Junin shekarar 2015. Boma boman an sarrafa su daga nesa a lokacin tawagar motocinsa take wucewa, tare da kuma jikkata masu tsaron lafiyarsa da dama.
A cewar binciken da jami'an tsaron cikin gida na Masar suka gudanar, wadanda ake zargin akwai yiyuwar sun samu tuntubar Hamas, kungiyar Falesdinu dake da cibiya a zirin Gaza. Tare da wasu manyan mambobin kungiyar 'yan uwa musulmi, sun shirya musammun ma kai hari kan manyan jami'an gwamnati, da nufin janyo baraka da hargitsi cikin kasa.
Tuhumar ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun samu horo a sansanonin soja na Hamas dake zirin Gaza mai makwabtaka, inda kuma suka samu boma boman da suka yi amfani da su wajen kai harin.
Kungiyar Hamas ta karyata sau da dama zargin cewa tana da hannu kan kisan Hisham Barakat, tare da tura wata tawaga a birnin Alkahira domin yunkurin maido da hulda tare da Masar, musammun ma ta hanyar fitar da sanarwowin sasantawa.
Mista Barakat ya gurfanar da miliyoyin magoya bayan tsohon shugaban kasa Mohamed Morsi, wanda ya fito daga kungiyar 'yan uwa musulmi, bisa dalilan janyo tashe tashen hankali da ta'addanci. (Maman Ada)