Bisa labarin da kafofin yada labaru na wurin suka bayar, an ce, a ranar 8 ga wata, dakarun dauke da makamai 4 sun kai hari ga wata motar 'yan sanda da ke garin Helwan da ke kudancin birnin Alkahira, inda suka harbe 'yan sanda 8 da ke cikin motar har lahira.
Ma'aikatar dake kula da harkokin cikin gida na kasar Masar ta sanar da cewa, a cikin wadanda suka mutu, akwai laftana guda da 'yan sanda guda 7, kuma suna cikin aikin sintiri a yankin kudancin birnin Alkahira a lokacin da lamarin ya faru.
Tun daga shekarar 2013, yankin zirin Sinai yana ta fama da tashe tashen hankali, inda dakarun dauke da makamai suke kai hare-hare ga 'yan sandan wurin, lamarin da zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar darurruwan mutane.(Bako)