in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban kwamandan sojin teku na kasar Sin ya ziyarci kasar Masar
2016-05-14 11:50:05 cri
Bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar Masar ya yi masa ne, janar Wu Shengli, babban kwamandan sojin teku na kasar Sin ya ziyarci kasar Masar tsakanin ranukan 10 da 12 ga watan Mayu.

A lokacin da yake ganawa da janar Sediqi Sobhi, ministan tsaron kasar Masar, janar Wu ya bayyana cewa, makasudin ziyararsa a kasar Masar shi ne neman kafa huldar "amincewa da juna, da yin hadin gwiwa irin ta a zo a gani cikin jituwa" a tsakanin rundunar sojin tekun kasar Sin da ta kasar Masar, ta yadda za a iya kai irin wannan hulda a wani sabon mataki. Janar Sobhi yana fatan za a iya yin hadin gwiwa a karin fannoni a tsakanin rundunonin sojin tekun kasashen biyu domin kafa wani sabon yanayi ga huldar dake tsakaninsu.

A lokacin kuma da yake yin shawarwari da takwaransa na kasar Masar Laftana-janar Osama El-Gendi a birnin Alexander, inda hedkwatar rundunar sojin tekun Masar take, janar Wu Shengli ya gabatar da shawarwari guda 4 kan yadda za a iya kafa huldar "amincewa da juna, da yin hadin gwiwa irin ta a zo a gani cikin jituwa" a tsakanin rundunonin sojin tekun kasashen biyu, da kara samun amincewa da juna cikin dogon lokaci. Da farko dai, janar Wu ya ce, kara ziyartar juna tsakanin manyan hafsoshin rundunonin biyu. Sannan kara yin mu'amala tsakanin jiragen ruwan soja na kasashen biyu. Bugu da kari, ya kamata a kara yin mu'amala tsakanin makarantun koyon ilmin rundunar sojan teku na kasashen biyu. Daga karshe dai, janar Wu yana fatan za a iya kara yin hadin gwiwa a wasu fannonin musamman na rundunar sojan teku.

A nasa bangare, laftana-janar Osama El-Gendi na kasar Masar ya tabbatar da kuma mayar da martani ga shawarwarin kara yin hadin gwiwa da janar Wu ya gabatar, yana fatan za a iya kara bunkasa huldar dake tsakanin rundunonin sojin teku na kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China