A yayin taron muhawara bisa taken " MDD, zaman lafiya, da tsaro" karkashin tsarin babban taron Majalisar a Talata, inda Jan Eliasson ya ce zaman lafiya da tsaron duniya na fuskantar babban kalubale. A cewarsa, yawan yake-yaken basasa da suka abku a wurare daban daban, ya ninka har sau 3 cikin shekaru 10 da suka wuce. Lamarin da ya sanya mutane miliyan 125 ke bukatar agaji. Kaza lika a cewar sa kashi 80% na irin wannan bukata na bulla ne sakamakon rikici, da matsalar sauyin yanayin duniya, gami da bala'i daga indallahi.
Za a kwashe kwanaki 2 ana gudanar da taron muhawarar, inda wakilan kasashe daban daban, ciki har da ministoci fiye da 20, za su bayyana ra'ayoyinsu dangane da matakan da MDD za ta iya dauka, don tinkarar kalubalen kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya.(Bello Wang)