Bisa yarjejeniyar, kasar Sin za ta samar da dalar Amurka miliyan 200 ga MDD a shekaru 10 masu zuwa, domin kafa asusuwan shimfida zaman lafiya da samun cigaba, wanda ke hade da sassa biyu, wato asusun zaman lafiya da tsaro na babban sakatare dake karkashin shugabancin ofishin babban sakataren MDD, da asusun tabbatar da ajandar neman dauwamammen cigaba nan da shekarar 2030, wanda ke karkashin shugabancin sashen dake kula da harkokin tattalin arziki da al'umma na MDD.
Kana MDD za ta kafa wani kwamitin ba da jagoranci ga asusun da zai hada da ma'aikatan Sin da na MDD a yayin da aka soma gudanar da aikin.
A yayin taron manema labaru da aka saba yi a wannan rana, kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya ce, babban sakatare Ban Ki-Moon ya yi godiya sosai game da gudummowar da kasar Sin ta baiwa majalisarsa, yana ganin cewa, wannan ya bayyana alkawarin da kasar Sin ta dauka kan goyon bayan manufar MDD da kuma ayyukanta.
A yayin da yake halartar jerin tarurrukan koli na cika shekaru 70 da kafa MDD, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, za a kafa asusun shimfida zaman lafiya da samun cigaba tsakanin Sin da MDD mai dauke da zunzurutun kudi har dalar Amurka biliyan guda, da nufin nuna goyon baya ga ayyukan MDD, da inganta harkokin hadin kai tsakanin bangarori da dama, hakan zai samar da sabuwar gudummawa ga tabbatar da zaman lafiya da cigaban duniya baki daya. (Bilkisu)