Kakakin MDD wanda ya bayyana hakan, ya ce an nada Patricia ce bayan wata tattaunawa da bangarorin da suka halarci wancan taro bayan tuntubar ofisoshinsu.
Epinosa Cantellano za ta maye gurbin Christiana Figueres 'yar kasar Costa Rica. Kafin wannan nada Episona Cantellano bisa wannan mukami ita ce jakadar kasar Mexico a kasar Jamus. Ta kuma rike mukamin ministar harkokin wajen kasar Mexico daga shekarar 2006 zuwa 2012, daga bisani kuma ta halarci taron kolin sauyin yanayi na MDD da ya gudana a shekarar 2011 a birnin Cancun na kasar Mexico.
A shekarar 1994 ne aka cimma yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD (UNFCCC) da nufin kimanta irin ci gaban da aka samu game da magance matsalar sauyin yanayi da ke addabar duniya.
A watan Disambar shekarar da ta gabata, kasashe 196 ne suka amince da wannan yarjejeniya, inda aka bukaci kasashen duniya da su rage fitar da iska mai gurbata yanayi da kasa da makin daigiri 2 na ma'aunin selsiyus.
Ya zuwa ranar 22 ga watan Afrilun wannan shekarar, kasashe 175 ne suka amince da wannan yarjejaniya a hedkwatar MDD. Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, ana bukatar kasashe 55 su goyi bayan wannan yarjejeniya ta Paris, wadanda bisa jimmala za su kai kashi 55 cikin 100 da ake bukata kafin ta fara aiki. (Ibrahim Yaya)