Ya ce, dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki domin yin amfani da karfin sojojin saman Nijeriya wajen kawar da 'yan kungiyar Boko Haram a jihar.
Bayan da sojojin sama sun jefa boma-bomai, an samu fashewar abubuwa a wurin, abun da ya shaida cewa, kila akwai makamai da harsashi a wurin. Kakakin ya kara da cewa, ci gaba da daukar wannan mataki, lamari ne da zai iya taimakawa wajen kawar da Boko Haram daga wurin.(Bako)