Mista Ban, ya furka hakan ne a lokacin da yake jawabi a dandalin taron MDD game da sha'anin cigaban tattalin arziki wato ECOSOC a takaice, yana mai cewa, an yi kiyasin ana bukatar kashe dalar Amurka trilliyan masu yawa a duk shekara domin aiwatar da wannan shirin.
Yace tattara wadannan makudan kudaden babban kalubale ne, bisa la'akari da yanayin rashin tabbas da tattalin arzikin duniya ke fuskanta a halin yanzu.
Shi dai shirin samun dauwamammen ci gaba na SDGs, ya kasance shiri na 17, wanda shugabannin kasashen duniya suka amince da shi a watan Satumbar shekarar bara, a matsayin wani jadawali da zai bunkasa cigaban kasashen duniya nan da shekaru 15 masu zuwa.
Mista Ban, yace zai yi amfani da wannan dama domin jan hankalin kasashen duniya da su kara yin hadin gwiwa wajen samar da kudaden shirin, domin inganata yanayin rayuwar alummomin kasashen duniya baki daya.
A watan Yulin 2015, kasashen duniya sun gudanar da taro a Addis Ababa, na kasar Habasha, domin amincewa da wani daftari game da yadda za'a samar da kudade da kuma aiwatar da shirin fasaha ta hanyar hadin gwiwa don raya cigaba mai dorewa.