Shugaban jam'iyyar mai mulkin kasar Pascal Nyabenda ya furta hakan ne a ranar cika shekara guda da bayyana shugaban kasar mai ci Pierre Nkurunziza a matsayin dan takarar zabe na jam'iyyar don neman wa'adin mulki karo na 3, lamarin da ya haifar da rikici da zanga zanga a fadin kasar.
Nyabenda ya fada cewa tattaunawar za ta duba yadda jam'iyyun siyasar kasar za su gyara kura kuran da aka tafka a lokacin zaben shekarar 2015.
Shugaba Nkurunziza yayi nasarar lashe zaben kasar a watan Yulin shekarar bara, bayan dakile wani yunkurin juyin mulki da bai samu nasara ba.
Sai dai 'yan adawa a kasar na zargin cewa, sake zaben nasa ya ci karo da dokokin kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya sahhale wa'adin mulki biyu na shugaban kasar kacal.
Sama da mutane 400 ne aka hallaka a lokacin zanga zanga a kasar ciki har da wasu manyan hafsoshin sojan kasar.(Ahmad Fagam)