in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta gudanar da bikin tunawa da ibtila'in filin wasa karo na 15
2016-05-11 16:38:08 cri
Kasar Ghana ta gudanar da bikin tunawa da mummunar annobar data faru a filin wasan kasar karo na 15, wanda ya haddasa mutuwar mutane 127 a birnin Accra a shekarar 2001.

Bikin wanda ya samu halartar jami'an gwamnati, da masu sha'awar wasanni, da kuma iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa dasu.

Yan wasa 127 ne suka hallaka a ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2001, a lokacin gasar wasannin firimiya ta cikin gida bayan da rikici ya kaure tsakanin 'yan wasan shahararrun kungiyoyin wasan kwallon kafan kasar biyu, wato Accra Hearts of Oak da kuma Kumasi Asante Kotoko.

Jami'an 'yan sandan kasar Ghana sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kafin su samu damar tarwatsa gungun masu rikicin, fadan dai ya barkene ne bayan da kungiyar wasa ta Hearts ta yi nasarar zara kwallaye 2, yayin da takwarar ta zara kwallo guda, lamarin da ya haddasa turmutsutsu a yayin da mutane ke kokarin tserewa daga filin wasan inda hakan ya zama ummul'abaisin da yayi sanadiyyar hasarar rayukan jama'ar.

Bayan ga wadanda suka mutu, daruruwa mutanene suka samu munanan raunuka a hadarin, wanda aka bayyana shi a matsayin hadari mafi girma da aka taba samu a filin wasa na nahiyar Afrika kuma shine mafi muni daya taba faruwa a tarihin duniya a karo na uku.

Ministan matasa da wasanni na kasar Nii Lantey Vanderpuije, ya jagoranci aza furannin tunawa da wadanda suka mutu a madadin gwamnati da alummar kasar Ghana, yayin da Kwasi Nyantakyi, shugaban kungiyar wasannin kwallon kafar Ghana ya jagoranci aza furannin a madadin kungiyoyin wasan kwallon kafan kasar.

Da yake gabatar da jawabi a lokacin bikin, Vanderpuije, ya bukaci kungiyoyin wasannin kasar dasu yi taka tsantsan wajen tada tarzoma a lokutan gudanar da wasanni.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China