Rangers dai ta lallasa Ikorodu United da ci 4 da 1, a wasan da suka buga ranar Lahadi, yanzu haka kungiyar na da maki 31 cikin wasanni 17 da ta buga.
Abia Warriors ita ke biye a matsayi na 2 da maki 30, bayan da ta samu nasara kan kungiyar Rivers United da ci daya mai ban haushi. A matsayi na 3 kuwa Kano Pillars ce, wadda ta tashi wasan ta da Heartland canjaras ba ci a gida. Yanzu haka Pillars din na da maki 28.
A wasan ranar Asabar mai rike da kofin gasar Enyimba ta doke FC Ifeanyi Ubah da ci 2 da nema. Sai dai duk da hakan Enyimba na matsayi na 8 a teburin gasar ta wannan kaka da maki 24 bayan buga wasanni 14, yayin da shi kuma kulaf din Ifeanyi Ubah ya kara yin kasa a kokarin sa na taka rawar gani a gasar.