in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Ekiti ta kafa kulob din kwallon kafa na mata
2016-05-19 09:20:45 cri
Hukumar wasan kwallon kafa ta jihar Ekiti dake tarayyar Najeriya, ta sanar da kafa sabuwar kungiyar wasan kwallon kafa ta mata mallakar jihar a birnin Ado-Ekiti, kungiyar da aka sanyawa suna 'Fountain Queens Football Club'.

Sanarwar da shugaban hukumar Ayodeji Alabi ya sanyawa hannu, ta nuna cewa an riga an kafa wani kwamiti na musamman mai kunshe da mutane 5, domin kula da harkokin kulob din don raya shi cikin sauri. Cikin sanarwar, Alabi ya ce babban burin hukumarsa shi ne samun wata kungiyar wasan kwallon kafa ta mata mai karfi a jihar. Za kuma a sanya 'yan mata masu sha'awar wasan kwallon kafa halartar kungiyar don takara da 'yan wasan mata na sauran jihohin kasar, in ji Alabi. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China