in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bremen ta doke Stuttgart 6-2 a gasar Bundesliga
2016-05-06 15:06:39 cri
Kungiyar Bremen FC ta kasar Jamus ta doke takwarar ta ta Stuttgart da ci 6 da 2, a wasan mako na 32 na gasar Bundesliga da suka buga a ranar Litinin.

Kulaflikan biyu dai na daf da tabbata a relegation, duba da tuni Bremen ta fada zuwa matsayin 16, yayin da ita kuma Stuttgart ke matsayi na 15. Duk da hakan, Bremen ta yi namijin kokari na lashe wannan wasa na ranar Litinin. Bisa hakan ne ma daraktan kungiyar Thomas Eichin, ke cewa kungiyar sa ta shirya matuka, kuma 'yan wasan sa sun maida hankali kwarai. Kuma bisa wannan nasara, Bremen ta tsallake matsayin relegation, inda a yanzu ta haye cikin jerin kungiyoyin gasar ta Bundesliga 15 mafiya yawan maki, yayin da ita kuma abokiyar karawar ta Stuttgart ta yi kasa zuwa matsayi na 17, wanda hakan ke nufin dai ta fada matakin na relegation.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China