151029-najeriya-za-ta-fara-wasannin-share-fagen-olympics-a-ranar-21-ga-watan-nuwamba-bello.m4a
|
Alhassan Yakmut, darekta janar na hukumar wasanni ta Najeriya, ya sanar da haka ne a yayin zantawarsa da manema labaru a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. A cewarsa, tsarin da za a bi wajen share fagen wasannin Olympics zai sha banban da fasahar da aka yi amfani da ita domin share fagen gasar All African Games.
Jami'in ya kara da cewa yanzu an riga an fara kokarin kulla kwantiragi tare da cibiyoyin horas da 'yan wasa daban daban don samar da dakunan wasanni ga 'yan wasan Najeriya ta yadda za su kimtsa sosai domin tunkarar wasannin Olympics da za a gudanar a Brazil a shekarar 2016.
Ban da haka a cewar mista Alhassan, a halin da ake ciki babu bukatar sanya 'yan wasan Najeriya su taru a wani wuri, sai dai za a kebe duk 'yan wasan kasar masu halartar wasannin Olympics cikin wata cibiya ta musammam dake birnin Rio a makwanni 2 kafin fara wasannin na Olympics.
Har ila yau, jami'in ya ce ana kokarin kimtsawa domin gudanar da wasanni raya al'adun gargajiya na kasar wadda aka shirya gudanarwa a bana amma daga bisani aka dage shi zuwa shekara mai zuwa.(Bello Wang)