in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwallon mata: Kamaru da Najeriya tana kasa tana dabo
2015-07-23 14:51:34 cri
Kulaf din kwallon kafar mata ta Najeriya wato Super Falcons, da takwarar ta ta Kamaru na cikin wani hali na ha'ula'i, a yunkurin su na shiga a dama da su a gasar nahiyar Afirka ta badi, bayan da kungiyoyin biyu suka buga kunnen doki a wasan share fage zagayen farko wasannin mako na 3, wanda suka buga a ranar Asabar.

Super Falcons ta Najeriya dai ta tashi kunnen doki 1-1 a wasan ta da Nzalang Nacional ta Equatorial Guinea, a filin wasa na birnin Abuja, yayin da ita kuma 'Les Lionnes' ta Kamaru ita ma ta tashi canjaras da takwarar ta ta kasar Ghana wato Black Queens, a filin wasa na birnin Yaounde.

Ana dai sa ran ganin kungiyoyin biyu sun taka rawar gani a wannan karo, duba da kasancewar su wadanda suka wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya ajin mata da ta gudana a 'yan makwanni da suka gabata a kasar Canada.

Idan dai ba a manta ba, Kamaru ta kai ga wasan zagayen karshe na gasar, duk da cewa karon farko da ta halarci gasar.

Game da yanayin da kulaf din ke ciki a yanzu haka, kocin Kamaru Enow Ngachu, wanda ya buga wasan na karshen mako ba tare da halartar wasu daga shahararrun 'yan wasan sa ba, saboda rashin dama daga kulaflikan 'yan wasan, ya ce yayi farin ciki da sakamakon, kuma 'yan wasan da ya buga wasan da su sun burge shi matuka, ya ma kara da cewa sa'a Ghana ta samu na cin kwallo daya a wasan.

A cewar Ngachu za su doke Ghana a gida, duba da cewa a baya Ghanan bata taba samun nasara kan Kamaru a birnin Accra ba.

Sai dai a nasa bangare kocin 'yan wasan Ghana Yussif Basigi, cewa ya yi yana fatan jagorantar 'yan wasan sa wajen kafa tarihi, na halartar gasar kasa da kasa a karon farko. Ya ce duk da girmama 'yan wasan na Kamaru da suke yi, hakan ba zai hana su fafatawa ba.

A wasan Najeriya da Equatorial Guinea na birnin Abuja kuwa, 'yar wasan Najeriya Halimat Ayinde ce ta fara bude ragar Equatorial Guinea cikin minti na 25 da fara wasan, kafin kuma Chinasa Okoro ta farke wannan kwallo a minti na 65.

A dai wasannin da aka riga aka buga, Afirka ta Kudu ce kadai ta samu cikakken maki 3, bayan da ta doke Kenya da ci daya mai ban haushi a filin wasa na birnin Johannesburg.

Ana sa ran kulaflika 2 da suka zamo zakaru a wasannin da ake bugawa, za su wakilci nahiyar a gasar birnin Rio de Janeiro, wadda za ta wakana tsakanin ranekun 3 zuwa 20 ga watan Agustar shekara mai zuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China