Jami'in ya ce abin mamaki ne ganin yadda wasu 'yan wasa suka janye jiki daga kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar a lokacin da suke da jinni a jiki. Ya jaddada cewa abin da kungiyar Super Eagles take bukata shi ne zama tsintsiya madaurinki daya, musamman ma ta la'akari da yadda kungiyar take kokarin farfado da yanayinta don komawa matsayi na daya daga cikin kungiyoyi wasanni mafiya karfi a duniya.
Mista Alhassan ya kara da cewa, ya kamata 'yan wasan na Super Eagles su sauke nauyin dake wuyansu, kuma a nan gaba ba za a yarda wani dan wasan ya nemi barin kungiyar ba tare da ya kwashe shekaru 10 yana taka leda cikin kungiyar ba. A cewar jami'in za a kaddamar da bincike kan 'yan wasan da suka yi ritaya don fahimtar dalilinsu, sa'an nan za a nemi hanyar da za a bi don daidaita batun.
Ban da haka kuma, Yakmut ya nuna yabo ga hukumar wasan kwallon kafa ta Najeriya, kan yadda kungiyar Super Eagles ta samu damar halartar gasar cin kofin zakarun Afirka ta 2016(CHAN). Ya yi alkawarin cewa hukumarsa za ta tallafawa kokarin kungiyar Super Eagles na neman lashe kofi a gasar da za ta gudana a kasar Rwanda.(Bello)