Kafin hakan Siasia ya riga ya gabatar da jerin sunaye mai kunshe da 'yan wasa 60 ga hukumar kwallon kafar Najeriya NFF, sai dai har ya zuwa yanzu yana ci gaba da kara wasu 'yan wasan cikin jerin sunayen, da nufin samun fitattun 'yan wasa mafiya dacewa, wadanda za su halarci wasannin Olympics a matsayin 'yan kwallon Najeriya.
Owolabi mai shekaru 21 a duniya, ya taba samun horo cikin kungiyar ta Najeriya kafin gasar All Africa Games ta shekarar 2015, da gasar AFCON ta 'yan kasa da shekaru 23, duk da cewa bai samu halartar gasannin ba a karshe, sakamakon yadda kulob din sa ya hana shi damar shiga gasar ta nahiyar Afirka.(Bello Wang)