in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihar Lagos za ta karbi bakuncin gasar motsa jiki ta Gymnastics
2016-05-05 18:54:51 cri
Jihar Lagos dake kudancin Najeriya, za ta karbi bakuncin gasar 'yan wasan motsa jiki na Gymnastics karo na biyu na wasu jihohin Najeriya, wadda za a gudanar tsakanin ranekun 10 zuwa 14 ga watan nan na Mayu, a rufaffen dakin wasanni na Mobolaji Johnson, dake filin wasa na Rowe Park a unguwar Yaba dake jihar ta Lagos.

A cewar kakakin hukumar wasannin jihar Titi Oshodi-Eko, an shirya gudanar da gasar ne domin kara bunkasa harkokin wasanni, tare da karfafa kwarewar 'yan wasan jihar, wadanda ka iya wakiltar jihar a gasannin kasa da kasa.

Har wa yau wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hakaito shugaban ta Adebamke Oloko na cewa, za a kara cikin nau'oin wasannin motsa jiki 24, kuma 'yan wasa daga jihohin kasar 6 ne ake sa ran za su hallara domin gwada basirar su.

Jahohin a cewar sanarwar sun hada da Lagos, da Oyo, da Delta, da Ekiti, da Ogun da kuma Ondo. Za kuma su aike da 'yan wasa 144 cikin ajujuwan gasar 3, wato ajin kwararru, da na matsakaita, da kuma na kanana. A karshen gasar dai za a baiwa mahalartan ta takardun shaidar shiga, da lambobin karramawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China