Shahararren dan wasan Tanis din nan Roger Federer, ya janye daga babbar gasar birnin Madrid ko Madrid Open, sakamakon ciwon da ya ji a kashin bayan sa, lokacin da yake atisaye a ranar Asabar.
Federer dai ya dawo wasa a gasar da aka fafata a Monte Carlo, bayan da ya sha fama da ciwo a gwiwar, ciwon da ya hana shi buga wasannin har kusan tsawon watanni 3.
Federer mai shekaru 34 da haihuwa, wanda kuma a baya ya lashe wannan gasa har sau 3, ya yi fatan samun sauki nan da dan lokaci, inda yake sa ran shiga gasar birnin Rome da za a yi a mako mai zuwa. Ya ce ko da yake yana samun sauki, amma ya fi son ya kara hutawa sosai, domin fuskantar gasar birnin Rome dake tafe, maimakon shiga gasar Madrid kafin murmurewar sa.
Federer dai shi ne na 3 a jerin 'yan wasan Tanis mafiya kwarewa a duniya, yanzu haka kuma yana shirin fuskantar manyan gasannin Tanis da ake yiwa lakabi da "Grand Slams" guda 3, da kuma gasar Olympics ta birnin Rio, wasannin da dukan su ke tafe nan gaba cikin wannan shekara.