in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar FIFA zai ziyarci Najeriya
2016-05-19 08:53:38 cri
Hukumar wasan kwallon kafar Najeriya NFF, ta sanar a ranar Lahadi cewa, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA, mista Gianni Infantino, zai ziyarci Najeriya a watan Yunin bana.

Sanarwar da mataimakin darekata mai kula da aikin hulda da manema labaru na hukumar NFF mista Ademola Olajire ya gabatar, ta ce ziyarar shugaban ta kasance daya daga cikin sakamakon da aka samu, yayin ganawar da shugaban na NFF Amaju Pinnick ya yi da Infantino a kasar Mexico a kwanakin baya.

An ce yayin ziyarar ta sa, shugaban FIFA zai gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, gami da kallon wasan karshe na gasar fidda gwani ta NFF/ZENITH Bank Future Eagles Championship. Ban da haka kuma, zai gana da shugabannin hukumomin wasan kwallon kafa na kasashen Afirka daban daban, wadanda za su isa Najeriyar don tarbar sa. Cikin sanarwar, an ce Infantino yana matukar gamsuwa kan yadda ake kokarin raya harkar kwallon kafar Najeriya da irin sha'awar da 'yan kasar ke nunawa kwallon kafa, yana kuma fatan mahukuntan kasar za su taimakawa kokarin hukumar ta FIFA, wajen raya wasanni a dukkanin fadin duniya baki daya. Kaza lika shugaban na FIFA yana farin cikin ganin yadda ake gudanar da ayyuka daban daban na horar da matasa a Najeriya, kuma bisa wannan dalili ne ya yi niyyar kallon wasan karshen da za a buga karkashin tsarin gasar NFF/ZENITH Bank Championship.

Mista Infantino ya fara zama shugaban hukumar FIFA bayan da ya ci zaben da aka yi a wani babban taron hukumar na musamman da aka kira a birnin Zurich na kasar Switzerland a ranar 26 ga watan Faburairun bana.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China