in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Arsenal ta kammala gasar Firimiya a matsayi na biyu, kana Manchester City ta samu gurbin buga gasar zakarun turai
2016-05-19 08:51:08 cri
Dan wasan Manchester City Kelechi Iheanacho, ya tallafawa kungiyar sa da kwallo daya a ragar Swansea, yayin wasan ranar Lahadi da kungiyoyin biyu suka buga, suka kuma tashi canjaras 1-1 a filin wasa na Liberty.

Da ma dai maki daya kacal Manchester City ke bukata, domin samun nasarar hana Manchester United shigewa gabanta a kakar wasa ta bana. Iheanacho dai ya taka rawar gani a kakar bana, inda ya ciwa Manchester City kwallaye 8 a gasar Firimiya, ciki hadda wannan kwallo daya da ta kasance mai muhimmanci ga Manchester City, duba da cewa da ita ne kungiyar ta samu damar kasancewa cikin kungiyoyi 4, da za su wakilci ingila a gasar zakarun turai da za a buga a kakar wasanni mai zuwa.

Ita ma kungiyar Arsenal ta gama kakar wasannin ta bana a matsayi na biyu, nasarar da rabon kungiyar da samun irin ta tun a shekara ta 2005. A wannan karo dai sun buga wasan su na karshe da Aston Villa, inda kuma suka samu nasara kan abokan karawar ta su.

A nata bangare kungiyar Leicester City wadda ta lashe kofin Firimiya na bana, ta kammala wasan ta na karshe kunnen doki da Chelsea. Lamarin da ya kara tura Chelsea kasan teburin gasar a matsayi na 10.

Everton kuwa ta doke Norwich, ko da yake hakan bai ba ta wata dama ta dagawa sama a teburin gasar ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China