Gano wannan abu wanda ya yi kama da wata nakiya mai fashewa, ya sa an dakatar da wasan da aka shirya bugawa tsakanin Man. United da AFC Bournemouth a Lahadin karshen makon jiya, aka kuma fidda 'yan kallo daga filin wasan na Old Trafford.
Cikin sanarwar da ya fitar, mataimakin shugaban ofishin 'yan sandan wurin, John O'Hare, ya ce bayan da aka yi bincike kan kunshin, aka kuma lalata shi a wani kebabben wuri, hakika kunshin wani kaya ne na wani kamfani mai zaman kansa, wanda ake amfani da shi don horas da karnuka masu sanssana nakiyoyi, wanda aka manta da shi cikin wani ban daki dake filin wasan.
Jami'in ya kara da cewa, ko da yake kunshin ba wani abun fashewa na gaske ba ne, amma siffarsa ta yi kama da ta wata nakiyar gaske, saboda haka kudurin da aka yanke na janye dukkan masu kallon wasa daga cikin filin ya dace ba kuma kuskure ba ne, domin ta haka ne kawai za a iya tabbatar da tsaron jama'a, in ji jami'in.(Bello Wang)