in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bayern Munich ta yi bikin lashe gasar Bundesliga a karo na 26
2016-05-19 08:52:46 cri

Kungiyar kwallon kafar Jamus Bayern Munich, ta yi bikin lashe gasar Bundesliga karo na 4 a jere, bikin da aka cashe a birnin Munich, a gaban masoya kungiyar a ranar Lahadin karshen mako.

Kimanin magoya bayan kungiyar 15,000 ne suka yi fitar dango domin taya 'yan wasan kungiyar, da jami'an ta murnar lashe kofin na bana. Bayan isowar tawagar 'yan wasan dauke da kofin ne aka ci gaba da shagulgula a unguwar Marienplatz, wurin da a ko da yaushe nan ne kungiyar ke murnar daukar kofunan da ta lashe. Su ma 'yan wasan kungiyar ajin mata sun shiga wannan biki, bayan da suma suka dauki kofin kalubale na kasar ajin mata.

Da yake tsokaci game da nasarar da suka samu, kocin kungiyar Josep Guardiola, wanda kuma ke daf da sallama da kungiyar bayan horas da ita tsawon shekaru 3, ya bayyana cewa a wannan kaka kungiyar na da damar lashe karin kofi a gasar German Cup a karo na biyu, yayin karawar da za su yi da Borussia Dortmund a wasan karshe, ranar 21 ga watan Mayun nan a birnin Berlin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China