in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da daya daga kososhin gwamnatin kasar Afghanistan
2016-05-17 21:05:41 cri

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da Abdullah Abdullah, daya daga cikin kusoshin gwamnatin kasar Afghanistan dake ziyarar aiki a nan kasar Sin.

Yayin zantawar su a babban dakin taron jama'a na kasar Sin dake nan birnin Beijing, shugaba Xi ya bayyana cewa kasar sa na gode wa Afghanistan, bisa goyon bayan da take nuna wa Sin a kan wasu manyan batutuwan dake shafar moriyar kasar Sin. Kasar Sin za ta ci gaba da goyon baya ga mulkin gwamnatin hadin kan al'umma ta kasar Afghanistan, tare da girmama tsarin siyasa da hanyar neman samun bunkasuwa da jama'ar Aghanistan suka zaba da kansu.

Ya ce kasar Sin na nuna goyon baya ga kokarin shimfida zaman lafiya da samun sulhu da jama'ar kasar Afghanistan suke yi, matakin da shi ne kadai zai tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A nasa tsokaci Abdullah Abdullah ya bayyana cewa, Afghanistan na godiya ga kasar Sin bisa taimakon da ta baiwa kasar sa lokacin da take fama da wahalhalu, da kuma goyon baya da Sin ta nuna wa gwamnatin hadin kan al'ummar Afghanistan. Kasar Aghanistan za ta ci gaba da kare matsayin da kasar Sin ke dauka kan wasu muhimman batutuwan da ke janyo hankalinta, ciki har da batun Taiwan. A daya bangaren Abdullah ya ce kasar sa tana fatan ci gaba da tuntubar kasar Sin, domin tabbatar da matsaya daya game da batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara hadin gwiwa tare da Sin a fannonin tattalin arziki, da manyan ayyukan yau da kullum, da harkar 'yan kwadago da kuma tsaro da dai sauransu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China