Mai rikon mukamin darektan tsare-tsare na hukumar samar da wutar lantarki ta kasar Kenya (KNEB)Winnie Ndubai ne ya shaida hakan ga manema labarai. Yana mai cewa, makamashin nukiliya ita ce hanya mafi dacewa ta samar da wutar lantarki da za ta taimakawa kasar Kenya wajen bunkasa harkokinta na tattalin arziki, don haka wajibi ne tsarin ya dace da yanayin kasar.
Hukumar samar da wutar lantarki ta kasar Kenya tana bukatar tashar samar da wutar lantarki da za a dogara da ita wajen samar da wutar lantarki nan da shekaru 20 masu zuwa.
A shekarar 2015 ne kasar Kenya ta bukaci hukumar kula da harkokin makashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) da ta gudanar da bincike kan shirinta na raya makashin nukiliya. (Ibrahim)