A yayin wani bikin konawa da ya gudana a ranar Asabar a Nairobi, babban birnin Kenya, kusan ton 105 na hauren giwa da ton 1.3 na kahon bauna aka kona domin yin kira ga duniya da ta kawo karshen kasuwanci na hauruna da kahonnin nau'o'in namun daji, lamarin da ke taimakawa wajen kawar da wadannan dabbobi daga doron duniya.
Bikin da aka shirya bisa jagorancin Kenya Wildlife Service, wata hukumar gwamnatin kasar dake kula da kiyaye muhallin daji, wannan biki ya gudana a gaban idon shugabannin kasashen Kenya, Gabon da Uganda, da kuma mataimakin daraktan zartaswa na tsarin kula da muhalli na MDD (PNUE), mista Ibrahim Thiaw, da kuma shugabar tsarin ci gaba na MDD (PNUD), madam Helen Clark.
Ba za mu rufe ido ba a ci gaba da farautar namun daji ba bisa doka ba har karin rana daya ba, in ji mista Thiaw a cikin wata sanarwa a wannan rana, tare da kara cewa, wannan ya sabawa duk wani tunani, tattalin arziki da siyasa. (Maman Ada)