Ibe Kachikwu wanda ya bayyana hakan a zauren majalisar wakilan kasar. Ya ce, aika-aikar tsagerun Niger Delta ta sa adadin man da kasar ta ke hakowa ta yi kasa daga ganga miliyan 2.2 zuwa ganga miliyan 1.4 a kowa ce rana.
Don haka ya bayyana kudurin ma'aikatarsa na ganin an gyara kayayyakin da aka lalata an kuma kare su yadda ya kamata.
Ministan ya kuma nanata bukatar gina kayayyakin more rayuwar jama'a, wadanda ya bayyana a matsayin ginshikin kara adadin danyen man da ake hakowa.
Rahotanni na nuna cewa, yau kusan shekaru 35 ke nan rabon a canja bututan man kasar, sannan matatun man na dab da tsayawa saboda tsufa.
Matasan da ke fasa bututan man a yankin Niger Delta dai na cewa, suna yin hakan ne saboda ba sa amfana daga kamfanoni da gwamnatin Najeriyar da ke hako albarkatun man da ke yankin nasu. (Ibrahim)