Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo ya tabbatar da hakan ne a jiya Litinin. Yana mai cewa, bai ji dadin yadda sojojin kasar suka ki yarda da kalaman nasa ba, duba da yadda 'yan tawayen na Avengers ke lalata batutan mai da ke yankin.
Don haka ya bukaci gwamnati da ta kaddamar da bincike don gano hakikanin wadanda suke da hannu wajen kafa sabuwar kungiyar tsagerun na yankin Niger Delta.
Bayanai na nuna cewa, sama da matasa 8,000 a yankin suka mika makamansu ga gwamnatin Najeriyar, a kokarin da ake yi na kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru ana tafbakawa a yankin mai arzikin man fetur.
Tun daga shekarar 2006 zuwa wannan lokaci, sama da 'yan kasashen waje 300 da ke aikin hako mai a yankin aka sace. Ko da ya ke an saki galibinsu bayan da aka biya kudin fansa.
Fasa batutan mai a yankin a 'yan shekarun nan, ya tilastawa Najeriyar rage kusan humusi na adadin man da take hakowa. Lamarin da ya sa mahukuntan kasar tura sojoji da masu gadin gabar teku don yakar wadannan bata gari. (Ibrahim Yaya)