Ministan harkokin kasashen waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ne ya bayyana hakan a Abuja, fadar mulkin kasar yayin taron koli kan harkokin tsaron shiyyar karo na biyu da ke gudana a kasar.
Ministan ya shaidawa manema labarai cewa, akwai kimanin mutane miliyan 2 da suka rasa matsugunansu da ke zaune a cikin kasar, baya ga kimanin yara 6,000 'yan kasa da shekaru biyar da aka raba da iyayensu batun da ministan ya ce wajibi ne a kalla da idon basira.
Ya ce, za a tantance kwayoyin halittan gadon yaran ta yadda zai dace da na iyayensu, kuma ta haka ne sauran kasashe ke bin diddigin 'yan ta'adda. Haka za a lika wannan mataki zai taimakawa kasar wajen tattara muhimman bayanai.
Ministan ya kara da cewa, taron kolin zai bullo da wani shiri game da ci gaban da aka samu bayan tashin hankali tare da bullo da karin matakan da za su tabbatar da cewa, nasarar da sojoji suka samu a yakin da suke yi da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin kasar ya yi tasiri a zukatan jama'a, ta hanyar sake gina kayayyakin more rayuka da mayar da su gidajensu yadda ya kamata. (Ibrahim Yaya)